fidelitybank

Katin Zabe: Tinubu ya yi amai ya lashe

Date:

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi amai ya lashe dangane da maganar da ya yi cewa wa’adin amfani da katin zabe ya kare, wato katin ya gama aiki.

A wata sanarwa da ofishin yada labarai na Tinubun ya fitar, ya ce, jagoran na su ya yi kuskuren ambaton kalmar karewa a Ingilishi wato ‘expire’ ne maimakon ya ce, ”kila akwai bukatar a sabunta katin.”

Sanarwar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da kalaman na Tinubu ne suka janyo har hukumar zabe ta Najeriya INEC, ta yi masa martani inda ta sheda wa BBC cewa wa’adin amfani da katin zaÉ“e bai Æ™are ba, za a ci gaba da amfani da shi wajen kaÉ—a Æ™uri’a.

Wani kwamishina ne a hukumar zaben bayan da BBC ta tuntube shi kan maganar ya faÉ—i hakan, bayan da wani bidiyo ya yaÉ—u a shafukan intanet da ke nuna Tinubu yana cewa wa’adin katin zaÉ“en ya Æ™are.

A cikin bidiyon an ga Bola Tinubu da takunkumi a fuskarsa kuma zagaye da mutane, ana jinshi yana cewa “wataÆ™ila ba za su gaya muku a kan lokaci ba… amma dai wa’adin amfani da katunan zaÉ“e ya Æ™are.”

Sai kuma Tinubu ya ci gaba da cewa: “kuna buÆ™atar yaÉ—a hakan a Æ™ananan hukumomi da mazaÉ“u komai wahalar yin hakan.”

A shekara ta 2021 ma a lokacin bikin cikar Asiwajun shekara 69 da haihuwa a Kano, jagoran na APC ya ce kamata ya yi a dauki matasa miliyan 50 a hukumomin tsaro na Najeriya domin shawo kan matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar, amma kuma daga baya ya ce kuskure ya yi yana nufin dubu 50 ne, bayan da kalaman nasa suka tayar da kura.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp