Kungiyar yan canji a jihar Kano ta ce daga yanzu za ta rika bude kasuwar hada-hadar canji daga karfe 12 na rana zuwa 6 na yammacin kowace rana.
Yan canjin da ke kasuwar wapa sun dauki matakin rage lokutan da kasuwar ke ci a wani bangare na nuna fushi da yadda farashin dala ke ci gaba da hauhawa.
Kungiyar ta ce za ta ci gaba da yin haka ne har sai farashin dala ya sauka.
A baya kungiyar tana bude kasuwar ne da karfe 8 na safe zuwa 9 na dare.
A yayin da kungiyar yan canji a Abuja, babban birnin Najeriya ta dakatar da hada-hadar musayar kudi har sai baba ta gani sakamakon karancin dala.
Yan Najeriya dai sun dogara kacokan kan kudin Amurka – dala domin tafiyar da harkokin da suka shafi kudi.
Abdullahi Dauran, shugaban yan canji a Abuja, ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne domin nuna wa yan Najeriya cewa sun damu da yadda ake samun karancin dala matsalar da ya dora kan ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kuÉ—aÉ—e ta Intanet irin na Crypto.
Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da Babban bankin Najeriya ke kokari na daidaita kasuwar musayar kudaden waje.
Babban bankin ya umarci bankuna su sayar da dala yau Alhamis tare da gargadin mutane kan boye dalar domin samun riba.