Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa NAHCON, ta ce, tana son sanar da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi, Ma’aikatu/Kwamishinoni, Masu Shawarwari da Lasisi, da sauran al’umma cewa, kason Alhazan da aka ware wa Najeriya gaba daya ya kare tun kafin yanzu.
A cikin wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, AD, mai kula da harkokin jama’a ta sanya wa hannu, hukumar ta ce, tana fatan daukacin manajojin aikin Hajji sun yi amfani da kason su bisa la’akari da yadda aka fara gudanar da aikin kamar yadda aka amince tun a fara gudanar da ayyukan.
Sai dai kuma ta ba da tabbacin cewa, idan Saudiyya ta mutunta bukatar ta na neman karin mukamai, hukumar za ta raba wa duk masu ruwa da tsaki da ke neman karin kaso ba tare da bata lokaci ba.
A halin da ake ciki, NAHCON ta bukaci daukacin hukumomin alhazai na Jihohi da masu zaman kansu da su kara mayar da hankali wajen shirya mahajjatansu, domin isar da su zuwa kasar Saudiyya kan lokaci.
Ta ce, bukatar a kwashe dukkan maniyyatan da suka yi rajista zuwa kasar lafiya kafin rufe sararin samaniyar Saudiyya, shi ne babban abin da ya fi daukar hankalin NAHCON.