Hukumar tabbatar da inganci kayayyaki a Najeria wato (SON) ta bayyana damuwa kan ƙaruwar shiga da kayayyaki marasa inganci a cikin ƙasar musamman na abinci.
Shugaban Hukumar, Malam Farouk Ali Salim, ya shaida wa BBC cewa, wannan matsalace babba saboda a yanzu duk kasuwar da aka je a Najeriya, idan ka dauki kaya kashi 8 a cikin 10 duk suna da matsala.
Ya ce ko ta wajen tantance kayan ko kuma lokacin amfaninsu ya kare, wanda hakan kuma zai iya sa tattalin arzikin kasar ya gamu da cikas matuƙar gwamnati ba ta ɗauki matakin daƙile matsalar ba.
”Abin damuwar shi ne yadda ake shigo da kayan abinci barkatai ba tare da an tabbabar da ingancinsu ba” in ji shi.