Mataimakin shugaban Najeriya ya sake jaddada kudurin goyon bayan masana’antun fina-finai na Kannywood da Hollywood da ke kasar.
Ya ce taron wanda shi ne na biyu a ‘yan kwanakin nan na da nufin nanata kudurin gwamnatinsu na sake fasalin bangaren shirya fina-finai da wakoki zuwa kan gaba a kokarin baza komar tattalin arzikin Najeriya.
Wata sanarwa da mataimakin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X, ta don tabbatar da hakan, gwamnatinsu ta kara kasafin kudin ma’aikatar raya al’adu da harkokin nishadi daga naira biliyan 1.1 zuwa naira biliyan tara.
Daga bangaren Kannywood, taron ya samu halartar jiga-jigan masana’antar kamar Ali Nuhu da Nuhu Abdullahi da kuma Mansura Isa.