Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya isa jihar Kaduna inda ya ziyarci asibitin koyarwa na Barau Dikko domin duba marasa lafiya da aka kwantar, cikin waɗanda harin jirgin sojin Najeriya maras matuƙi ya raunata.
A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgi maras matuƙi na sojin Najeriya ya jefa bam ‘bisa kuskure’ a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Shettima wanda ya isa jihar ta Kaduna a yau Alhamis, ya ziyarci ɗakunan majinyata na asibitin, tare da rakiyar gwamnan jihar, Uba Sani, domin duba waɗanda aka kwantar.
A lokacin ziyarar tasa ya tabbatar wa marasa lafiyar cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata wajen tallafa musu.