fidelitybank

Kashi na biyar daga Ukraine sun dawo Najeriya

Date:

Kashi na biyar na ‘yan Najeriya da aka kwashe daga kasar Ukraine sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da sanyin safiyar Juma’a.

Sun isa ne a cikin wani jirgin sama mallakin Air Peace, daya daga cikin kamfanonin jiragen da aka biya kudin jigilar ‘yan Najeriya da suka dawo daga Ukraine. An dauke su ta jirgin sama daga Poland inda suka gudu bayan yakin Ukraine.

An kwashe ‘yan Najeriya 123 a jirgi na biyar, a cewar gwamnatin tarayya.

Mutanen da aka kwashe, a cewar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), sun kuma samu katin SIM na kyauta wanda aka yi ma su da lokacin isar da sako domin su samu damar isa ga ‘yan uwansu ta hanyar hadin gwiwa tsakanin NiDCOM da MTN.

Wadanda aka kwashe sun kuma karbi dala 100 na sufuri kamar yadda ma’aikatan da suka iso gabansu suka samu.

A ranar Asabar ne ake sa ran wani rukunin zai isa Najeriya daga kasar Hungary, kamar yadda wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.

PREMIUM TIMES ta ruwaito isar mutane 1,078 da suka isa Najeriya a makon da ya gabata ta hanyar Max Air da Air Peace, kamfanonin jiragen biyu sun dauki nauyin jigilar ‘yan Najeriya da suka dawo daga Ukraine.

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp