Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, sun ce ƴanbindiga sun kashe jami’an da ke samar da tsaro goma sha uku (13) a cikin mazabar Adabka, yayin da suke tsaka da gudanar da sintiri.
Harin wanda ƴanbindigar suka kai a jiya Juma’a, sannan suka ƙi bari a shiga domin a kwaso gawarwakin jami’an da suka kashe domin yi musu sutura.
Hamisu A Faru, shi ne ɗan majalisar jihar, mai wakiltar Bukuyum ta Kudu, a zantawarsa da BBC ya buƙaci gwamnatin tarayya ta gaggauta kai musu ɗauki, bisa la’akari da girman matsalar.
Ya ce al’ummar mazaɓarsa na cikin tashin hankali, “musamman ganin waɗanda suke taimaka musu wajen ba su kariya ne aka kashe. Ka ga ke nan me ya rage? ai sai gudun hijira, dama tuni wasu sun gudu zuwa Zuru.”
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa kashi 70 na mazaɓar Bukuyum ta Kudu, a ƙarƙashin mulkin ƴanbindiga yake.
A ƙarshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tura jiragen yaƙi a shiga dazukan, “a yi luguden wuta sansanonn ƴanbindigar.”