Gwamnatin ta bayyana cewa, kashi 63 cikin 100 na ƴan ƙasa, wato mutum miliyan 133 na cikin talauci.
Alƙaluman binciken ma’aunin talauci a Najeriya ne suka tabbatar da hakan a yau Alhamis a Abuja.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa da hukumar tsara bayar da tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi da shirin samar da ci gaba na majalisar ɗinkin duniya da asusun ilimin ƙanana yara na Unicef da shirin yaƙi da talauci da cigaban al’umma na Oxford ne suka gudanar da aikin ƙididdigar.
Binciken ya nuna cewa an karɓi bayanan magidanta dubu 56 a sassan jihohin ƙasar 36 da birnin tarayya Abuja, da aka gudanar tsakanin watan Nuwamban 2021 zuwa Fabarairun 2022.
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matalauta a ƙasar na rayuwa ne a arewacin Najeriya, yayin da kashi 35 cikin 100, kusan mutum miliyan 47 ke nan na zama ne a kudanci.
Sokoto ce jihar da ta fi fama da talauci a ƙasar, inda kashi 91 cikin 100 na al’ummarta ke rayuwa hannu-baka hannu-ƙwarya, Ondo ce kuma mafi ƙarancin talauci a Najeriya da kashi 27 cikin 100.
A lokacin da ya yi tsokaci kan alƙaluman, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wannan bayani zai bijiro da hanyoyin da za a bi wajen yaƙi da talauci.