Wani sabon rahoton da cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da hadin gwiwar ƙungiyar Afirka, sun ce ‘yan Afirka miliyan 282, kusan kashi 20 na al’ummar nahiyar ne ke fama da matsalar ƙarancin abinci.
Rahoton haɗin gwiwar ya kuma nuna cewa yawan mutanen da ke fama da ƙarancin abinci sun ƙaru da miliyan 57 tun bayan ɓarkewar cutar covid, lamarin da ya haifar da taɓarɓarewar matsalar abinci a nahiyar.
“Mafi yawan al’ummar Afirka – kusan kashi 78 ko fiye da mutum biliyan guda – ba sa samun lafiyayen abinci, idan aka kwatanta da kashi 42 da ke samun hakan a faɗin duniya, kuma adadin na ci gaba da ƙaruwa,” in ji rahoton.
Rahoton ya kuma alaƙanta rashin samun lafiyayen abincin kan matsalar ƙarancin abinci da aka fuskanta a ‘yan shekarun baya-bayan nan, musamman a Yammaci da Gabashin Afirka, wanda ya sa ba ma talakawa kaɗai ba, har ma da masu dama-daman ba sa iya samun lafiyayyen abinci.
Hukumomin sun kuma ce kusan kashi 30 na ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekara biyar ne a nahiyar suka takure sakamakon rashin samun ingantaccen abinci.