Kwamitin Majalisar wakilai da ke sa ido kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati ya gayyaci ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 63, domin bayar da bahasi game da aiwatar da wasu ayyukan da ba sa cikin kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar a gaban majalisar, abin da kwamitin ya ce ya haddasa kashe kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da yawansu ya kai sama da tiriliyan biyu.
Shugaban kwamitin Oluwole Oke, ya rubuta wasiƙa zuwa ga babban daraktan hukumar kasafin kuɗi ta ƙasar yana mai bayyana buƙatar neman hujjar majalisar wakilan kasar kan yin hakan.
Shugaban ƙasa ne ke miƙa kasafin kuɗin ma’aikatu ga hukumomin gwamnatin zuwa ga majalisar wakilan ƙasar, yayin da Akawun majalisar zai mayar wa shugaban kasar kasafin da majalisar ta amince da shi domin aiwatarwa.
Yayin da yake ƙarin haske kan wasiƙar mista Oke ya ce ”An kashe sama da tiriliyan biyu ba bisa ƙa’ida ba. Shugaban ƙasa bai kawo kasafin kuɗinsu ba. Dole su faɗa wa ‘yan Najeriya me yasa suke aiwatar da kasafin kuɗin da bai bi matakan shari’a ba”.
”Shugaban ƙasa bai gabatar da kasafinsu a majalisa ba. Haka kakakin majalisa da shugaban majalisar dattawa ba ɗaya daga cikinsu da ya gabatar da wannan batu a harabar majalisun dokokin ƙasar biyu. Dan haka mun gayyaci hukumomin da su zo su yi bayani”, in ji shi.