Ƙasashen Yamma za su jawo “haɗari mai girma” idan suka bai wa Ukraine jiragen yaƙi na F-16, a cewar Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha Alexander Grushko kamar yadda kamfanin labarai na TASS ya ruwaito.
Ya yi martanin ne bayan Amurka ta ce ba za ta hana ƙawayenta su bai wa Ukraine ɗin jiragen da ta ƙera ba da kuma bai wa sojojin ƙasar horon yadda za su yi amfani da su.
“Mun ga yadda har yanzu ƙasashen Yamma ke bin hanyar rura wutar. Za su jawo wa kansu haɗari mai girma,” in ji Grushko.
“Ko ma dai mene ne, za mu saka wannan cikin tsare-tsarenmu, kuma muna da dukkan abubuwan da muke buƙata don cimma muradanmu.”