Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya yi gargadin katsalandan daga kasashen waje a zaben 2023 a Najeriya.
Ya yi wannan gargadin ne a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja a yayin wani liyafar buda baki da jami’an diflomasiyya.
Ya ce, “Kamar yadda kuka sani, wa’adin wannan Gwamnati zai kare ne a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. Yawan shekarun zabe a duk fadin duniya, lokutan harkokin siyasa kan yi yawa.
”Haka ne yanayin dimokuradiyya. Na kuduri aniyar baiwa Najeriya kyakkyawar al’adar sahihin zabe fiye da yadda na hadu da ita.
“Yayin da Najeriya ke cikin wannan hali, ina kira ga abokanmu na duniya, wadanda kuke wakilta, jami’an diflomasiyya, da su yi aiki mai kyau da ke karfafa rukunan mutunta al’amuran cikin gida da mutunta gaskiya ba tare da an riga an yi tunani da son zuciya ba.”
Buhari ya sha alwashin yin amfani da duk wata halastacciyar hanya, don kare kuri’un ‘yan Najeriya a zaben 2023.