Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya Fifa, Gianni Infantino, ya zargi ƙasashen Yamma da “munafurci” game da rahotannin da suke bayarwa na Kofin Duniya da za a yi a Qatar.
Yayin wani taron manema labarai a yau Asabar a birnin Doha na Qatar, Infantino ya kare ƙasar game da abin da ya kira ci gaban da ta samu game da zarge-zargen da ake yi mata.
Ya fara da cewa: “Yau ina jin ni ɗan Qatar ne, ina jin ni Balarabe ne, ni ɗan Afirka ne, ni ɗan luwaɗi ne, ni mai nakasa ne, ni ɗan cirani ne.”
Ya ƙara da cewa: ” Ni bature ne. Abin da muka shafe shekara 3,000 muna aikatawa a faɗin duniya, ya kamata mu shafe wasu 3,000 ɗin muna neman afuwa kafin mu yi wa wani wa’azi.
“Irin wannan wa’azin na ɓangare ɗaya munafurci ne. Ina mamakin yadda mutane suka ƙi magana game da ci gaban da aka samu a nan tun daga 2016.”
A gobe Lahadi za a take wasan farko a gasar ta Kofin Duniya, lokacin da Qatar za ta fafata da Ecuador a filin wasa na Al Bayt da ƙarfe 5:00 na yamma a agogon Najeriya da Nijar.