Ministocin harkokin waje na ƙasashen Larabawa za su gana a birnin Doha na Ƙatar ranar Talata, inda ake sa ran za su yi muhawara kan yaƙin Isra’ila a Zirin Gaza.
Haɗuwar na zuwa ne mako uku bayan shugabannin ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun tattauna a Saudiyya kuma suka nemi tsagaita wuta nan take a Gaza.
Mazauna ƙasashen nasu na goyon bayan Falasɗinawa sosai a wannan rikici kuma shugabannin na shan matsi daga ‘yan ƙasar tasu don su ɗauki tsattsauran mataki kan Isra’ila.
Kusan dukkan ƙasahen Larabawa da suka gyara alaƙa da Isra’ila sun janye jakadunsu daga ƙasar bayan luguden wutar da ta fara a kan Gaza ranar 7 ga watan Oktoba – bayan harin Hamas da ya kashe mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da wasu fiye da 200.
Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe sama da mutum 15,200 a hare-haren da take kaiwa a Gaza tun daga ranar, 6,000 daga cikinsu yara ne ƙanana, kamar yadda ma’aikatar lafiya a Gaza ta bayyana.


