Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Afganistan ta ce abu ne mai matukar wuya ƙasashen duniya su amince da gwamnatin Taliban matukar ta ci gaba da taƙaita ƴancin mata.
Roza Otunbayeva ta shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa matakan da gwamnatin Taliban din ta dauka na iyakance damarmakin mata, ba su samu amincewa ba a wajen ‘yan kasar.
Ta ce a tattaunawar da ta sha yi da shugabanninsu, ta fito karara ta nuna musu irin matsalolin da suka haifar, da yadda suka jefa rabin al’ummar ƙasar cikin wahala, da lalata tattalin arziƙin ƙasar.
Yanzu haka an haramta wa mata yawancin ayyuka, da kuma zuwa wuraren taruwar jama’a, kamar makarantu da wuraren shaƙatawa.
‘Yan Afganistan sun fuskanci matsalar jin kai mafi girma a duniya tun bayan da Taliban suka kwace iko da su kusan shekaru biyu da suka gabata.


