Ministan harkokin wajen Isra’ila, Katz, ya ce, yana jagorantar wani shiri na neman ɗaukar mataki kan Iran a difilomasiyyance bayan harin da ta kai mata.
Israel Katz, ya bayyana hakan ne yayin da gwamnatin ƙasar ke duba yiwuwar mayar da martani kan harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ta kai mata ranar Lahadi.
Isreal Katz ya aika takarda ga ƙasashe da dama, inda yake neman su ƙaƙaba wa Iran takunkumi kan shirin ƙera makamai masu linzami na Iran.
Ya kuma yi kira da a ayyana dakarun juyin juya halin Iran a matsayin ƙungiyar ta’addanci a matsayin wata hanya ta yaƙi da kuma rage wa Iran ƙarfi.
Ya ƙara da cewa, dole ne a dakatar da Iran a yanzu, kafin lamari ya ɓaci.