Kamaru wacce ta lashe gasar sau biyar, ta samu katin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025.
Hakan ya biyo bayan nasarar da suka samu a kan Kenya da ci 1-0 ranar Litinin, inda Boris Enow ya zura kwallo daya tilo a karawar da suka yi a Kampala.
Zakarun na 2019 Aljeriya ma ta samu tikitin shiga gasar.
Desert Foxes ta doke Togo da ci 1-0 a Lome, sakamakon bugun daga kai sai mai tsaron gida Ramy Bensabaini.
Wannan ya kawo adadin kungiyoyin da suka cancanta zuwa hudu.
Kamaru da Aljeriya sun bi sahun masu masaukin baki Morocco da Burkina Faso kamar yadda kungiyoyi hudu suka tabbatar da zuwa wasan karshe.