Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasa na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.
A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.
Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.
Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.


