Mutane uku sun rasu yayin da wasu kuma suka jikkata a wani hadarin zaftarewar kasa da ya faru a yankin Keffi na jihar Nasarawa.
Shugaban Karamar Hukumar ta Keffi, Muhammad Baba Shehu ya tabbatar da hakan a wata hira da BBC.
Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Talata a lokacin da mutanen ke hakar yashi a wani wurin É—ibar yashi da ke unguwar Ayaba.
Nasarrawa na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda ke da arziƙin albarkatun ƙasa.
HaÆ™ar ma’adanai ba bisa Æ™a’ida ba abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da a lokuta da dama kan haifar da mutuwar mutane saboda rashin É—aukar matakan kariya da suka kamata.