Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta cafke wani mai tuƙa babur ɗin Adaidaita sahu Yusuf Abdurrahman Ƙwaya bisa zargin sa da satar wayoyin mutane a babur ɗinsa.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa ya raba wa manema labarai da yammacin yau Litinin.
Sanarwar ta ce, jami’an hukumar ne suka cafke matashin a kan Titin Yan kaba.
saƙon murya da jami’i ya raba wa manema labarai ya ce,, Yusuf Abdurrahman mai laƙabin Ƙwaya da aka cafke shi bisa zargin satar wayoyin ya ce, “Ba ƙwace muke yi ba kwai ƴan dabaru muke yi wajen ɗaukar wayoyin”.
“Wani lokacin muna yaudarar mutane da cewa za mu sayi ruwan sha ko kuma mu yi musu wata dabarar, wannan shi ne karo na biyu da aka taɓa kama ni ana kawo ni hukumar KAROTA” Inji shi.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauke wa waya Malam Rabi’u Ya’u ya shaida wa hukumar ta KAROTA cewa, “Na hau babur ɗin ɓata garin ne daga tashar ƴan Kaba, kuma bayan ya hau ne sai abokin tafiyar direban ya sauya mazauni daga kusa da shi zuwa gaban baburin kusa da direba”.
“Ashe ban sani ba tun lokacin da ya sauya wurin tuni ya sace mun waya, don haka da suka tsaya zan sauka ba su tsaya na ba su kuɗi ba suna ta sauri sai da kyar na ba su, daga nan ne ban ga waya ta ba, don haka na yi ta kiranta m, sai dai daga bisani aka ɗaga tare da faɗa mun na zo gidan KAROTA na karɓa an kama su”.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa tuni hukumar ta miƙa Yusuf Ƙwaya ga rundunar ƴan sanda ta jihar Kano domin faɗaɗa bincike tare da wayoyin da aka cafke shi da su guda shida. In ji jaridar Kakaki.