fidelitybank

Karo na Farko: Gwamnatin Kano ta magantu a kan Sarauniyar Kyau

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta magantu a kan shirun da ta yi dangane da cece-kucen da ya biyo bayan sarauniyar kyau ta shekarar 2021 a Najeriya Shatu Garko mai shekaru 18 wadda ta lashe kyautar a jihar Legas.

Gwamnatin jihar ta ce ba ta da masaniya game da halartar ta ko kuma yadda lamarin ya faru.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kwamared Muhammad Garba, ya bayyana matsayin gwamnati a lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu a Kano.

Ya ce,”‘Yar takarar ba ta sanar da gwamnatin jihar a hukumance ta shiga gasar ba, kuma ba za ta san yadda lamarin ya kasance ba”. Inji Kwamrade.

Da a ka tambaye shi ko za a yi mata liyafar tarba na musamman na jan kafet, Muhammad ya ce: “Mun ga labarin ne kawai a shafukan sada zumunta game da labarin gaba daya. Ba zan iya bayyana ra’ayin gwamnatin jihar kan ko za a yi liyafar jan kafet ko kuma a’a a duk lokacin da ta nuna sha’awarta ta zuwa Kano kamar yadda wasu fitattun jarumai da su ka jawo wa jama’a daraja su ke yi. A gaskiya ban san komai ba game da wannan lamarin”.

“Za mu mika wannan batu zuwa ga kwararrun mahukunta na Musulunci da kuma manyan malaman Musulunci, domin jin ta bakinsu da kuma abin da Musulunci ya ce, game da wani labari mai girman gaske. Idan a ka yi haka ne za mu iya fito da matsayarmu ta karshe kan abin da ka iya faruwa,”

Kwamishinan ya kara da cewa. “Misali hukumar Hisbah mai zaman kanta a Kano, an rawaito cewa ta gayyaci iyayenta domin tambayar su a kan wannan lamari”. A cewar Kwamrade Muhammad Garba.

Matashiyar ta kafa tarihi a daren Juma’a a lokacin da ta zama mace ta farko mai sanye da hijabi da ta lashe gasar Miss Nigeria.

Matashiyar wadda ta kasance mai son hawan dawakai mai shekaru 18, wanda a ka ce shi ne mafi karancin shekaru a gasar bana, da ta zo na daya bayan da ta doke sauran ’yan takara 18 da ta zama mace ta 44 ta Miss Nigeria.

Wadda ta lashe zaben kuma ta wakilci shiyyar Arewa-maso-Yamma a wajen taron wanda a ka gudanar a Landmark Centre, Victoria Island a jihar Legas tare da Nicole Ikot da Kasarachi Okoro sun zama na daya da na biyu a matsayi na biyu.

Domin cimma wannan nasarar, Miss Garko ta samu kyautar Naira miliyan 10, da zama na shekara a wani katafaren gida da sabuwar mota da sauran damammaki na jakadanci da ta samu.

Sai dai fitowar Shatu ya haifar da fushin jama’a daga Kano, wanda jiharta da kuma martani daga wasu malaman addinin Musulunci.

 

 

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta...

Za afara rijistar masu zabe a Najeriya – INEC

Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin...

Ma’aikatan Jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma'aikatan jinya da...

Izak ya na ɗaukar horo bayan ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana...

Masu tsaigunta wa ƴan Bindiga ne ke haddasa kashe-kashe – Gwamnan Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga...

Gwamnoni ku yi wa mutanen ƙauyika da karkara ayyuka – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su...

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...
X whatsapp