Shugaban Amurka, Joe Biden, ya tattauna da takwaransa na China, wani abu da ke nuna dawowar ƙyaƙƙyawar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.
Mista Biden da Xi Jinpin sun yi musabaha cikin raha a farkon haɗuwarsu a Bali gabanin taron manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G20 da za a gudanar a wannan shekarar.
Shugaba Biden ya ce bai kamata ƙasashen biyu su bari gogayya ta kai su ga rikici ba.
A nasa ɓangaren, Mista Xi ya ce duniya na fatan ganin alaƙarsu tana tafiya dai-dai.