Wasan ƙarshe na gasar FA ta wannan karon da za a yi a ranar 3 ga watan Juni za a fara shi ne da misalin ƙarfe 3 na ranar, karon farko cikin shekara 12.
Wasan da za a fafata tsakanin Manchester Uinted da Manchester City a filin wasa na Wembley an saba gudanar da shi ne tsakanin 16:45 da 17:30
Amma jami’an Landan sun ce wasan na hammaya ne mai cike da hatsari, kuma zai iya zama barazana ga tsaro idan aka yi shi da daddare.
Wannan ne karon farko da za a fara wasan da misalin arfe uku na rana tun wanda aka yi a 2011, tsakanin Manchester City da Stoke.
Wannan ne karon farko na wasan tsakanin Manchester, an bai wa Liverpool da Chelsea damar kujera 30,000 a wasan.