Dazun mun kawo labarin cewa mutum shida sun kaɗa ƙuri’a a New Hampshire na Dixville Notch, inda wurin ne aka fitar da sakamakon zaɓen Amurka na farko a tsakar dare. Trump ya samu ƙuri’a uku, Kamala ta samu uku.
Wakilin BBC ya zanta da wani wanda ya zaɓi Democrats a karon farko a yankin mai suna Les Otten, inda ya ce ya zaɓi Harris ne saboda ta san ƙokarin mutane, kuma ta yarda akwai rawar da mutane za su taka a gwamnatin.
“Idan wanda aka zaɓa ya fahimta tare da aminta cewa dukkanmu muna da rawar da za mu taka a gwamnati, ai wannan ya fi muhimmanci.”