fidelitybank

Karin albashi mafi karanci zai fara aiki ranar 1 ga watan Afirilu – Gwamnatin Tarayya

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce, sabon tsarin mafi karancin albashi zai fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Afrilun 2024.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasar, Idris Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar PUNCH a Abuja, ya ce tsarin mafi ƙarancin albashi na naira 30,000 na yanzu zai daina aiki ne a karshen watan Maris na shekarar 2024.

Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin nazarin kasafin kudi na shekarar 2024-2026 da shugaba Tinubu ya gabatar inda ya ce za a kashe naira tiriliyan 24.66 kan albashi a shekarar 2024 da 2025 da kuma 2026.

Bayan cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, gwamnatin tarayya ta amince ta bai wa kowane ma’aikacinta tallafin naira 35,000 domin rage raɗaɗin cire tallafin.

Sai dai kungiyar ƙwadago ta dage kan cewa tallafin naira 35,000 na wucin-gadi bai wadatar ba, inda ta kara da cewa ya kamata a sake duba mafi karancin albashi a shekarar 2024.

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tattaunawar Ma’aikata ta Kasa a ranar 18 ga Oktoba, 2019, sun amince da aiwatar da mafi karancin albashi na naira 30,00 bayan shafe watanni ana tattaunawa.

Sai dai a ranar Alhamis kungiyar kwadago ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da gwamnatin tarayya, inda ta kara da cewa bisa tsarin dokar kwadagon kasar ya kamata a sake duba mafi karancin albashi duk bayan shekaru biyar.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya ce kwanan nan, “Sake duba mafi ƙarancin albashi na kasa lamari ne na doka da ake sa ran zai faru a 2024.”

A nasa ɓangaren, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed, ya shaida wa jaridar PUNCH cewa, ƙarin albashin na da nufin maye gurbin matakin wucin-gadi da gwamnati ta sanya don magance wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp