Kwamanda, wato karen Shugaban Amurka, Joe Biden ya ciji jamiāan Hukumar tattara bayanan sirri na Amurka akalla sau 24, kamar yadda sabbin takardu suka nuna.
Bayanan sirrin Amurka sun nuna yadda karen – wanda daga Jamus aka samo shi – ya haifar da fargaba tsakanin masu tsaron fadar shugaban kasar.
Lamarin da ya haifar da sauye-sauyen dabarun tsaron fadar shugaban kasar.
Wani babban jami’in ya lura cewa cizon ya haifar da gyare-gyare a cikin dabaru, tare da shawarwari.
Lamarin ya faru ne tsakanin Oktoban 2022 da Yuli 2023, wanda ya yi sanadin jikkatar jami’in tsaron a sassan jikinsa daban-daban.
Takardun, wadanda aka samu ta hanyar bukatu na āYancin Bada Labarai, sun nuna irin munin cizon da jami’in ya samu, wanda ya sa aka tsige karen daga Fadar White House a watan Oktoban bara.