Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana wasansu na zagaye na biyu na gasar zakarun Turai da Real Madrid a matsayin wasan “karshe”.
Zakarun gasar firimiya ta buga wasa mai ban sha’awa 3-3 da Los Blancos a ranar Talatar da ta gabata.
Gabanin karawar da za a yi a Etihad a wannan Laraba, Guardiola na fatan samun mai tsaron baya Kyle Walker a karawar.
“Kyle Walker yana jin dadi sosai, watakila zai iya taimakawa da mintuna da Real Madrid saboda wasan karshe ne.
“Amma ba na son in rasa shi na dogon lokaci… za mu yanke shawara a cikin kwanaki masu zuwa.”
Walker bai buga wa City wasa ba tun lokacin da ya samu matsalar tsoka a lokacin hutun kasa da kasa na karshe.