Gwamnan jihar Ondo ya ƙara jaddada matsayar gwamnonin Kudu cewa, wajibi ne a baiwa ɗan Kudu kujerar shugaban ƙasa a 2023.
Rotimi Akeredolu, ya ce, matukar a na son yin adalci da kuma dai-daito to bayan shekara 8 a Arewa kamata ya yi mulki ya koma Kudu.
Ya ce gwamnonin Kudu sun riga sun yanke hukunci, duk wanda a ka tsayar daga yankin Kudu to shi za su zubawa ruwan kuri’u.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, shugaban ƙungiyar gwamnonin Kudu kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu (SAN), ya yi wannan furucin ne a ofishinsa, yayin da ya karɓi baƙwancin kungiyar Power Rotation Movement, bisa jagorancin shugaba, Dr. Pogu Bitrus.