fidelitybank

Karancin man fetur ka iya janyo tashin farashin kayayyaki

Date:

Shugaban Sashen Ƙididdiga na kasa, Dr Simon Harry, ya ce, ƙarancin man fetur da ake fama da shi a wasu sassan ƙasar nan, zai iya shafar hauhawar farashi a watan Fabarairu idan ba a ɗauki mataki ba.

Da ya ke jawabi a wurin taron manema labarai a ranar Talata, Dr Harry, ya ce, ƙarancin man zai haifar da fargaba kan tattalin arziki ta yadda farashin kayan abinci za su tashi da kuma ladan ayyuka.

Ya kuma ce ko a na so ko ba a so, masu safarar kaya za su yi amfani da wannan damar wajen ƙara kuɗin dako.

Dailytyrst ta rawaito cewa, Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce, an samu raguwa a hauhawar farashin kaya a Najeriya a watan Janairun da ya gabata da kashi 0.34 cikin 100 idan aka kwatanta da Disamban 2021.

Yanzu haka dai ana sayar da lita ɗaya ta man fetur ɗin kan kai Naira 500 ko fiye a Abuja, yayin da gidajen mai ƙalilan ne ke sayar da man.

A gefe guda kuma, kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya ce, ya bayar da umarnin dakon mai daga manyan rumbuna da kuma sayar da shi a gidajen mai a fadin kasar, ba dare ba rana a kokarin kawo karshen matsalar.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar jiya Talata, NNPC ya ce yana ba wa ‘yan kasar tabbacin daukar matakan da suka dace domin hanzarta samar da man a fadin kasar.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp