fidelitybank

Karancin kudi zai kawo cikas wajen kidayar ‘yan Najeriya – Agba

Date:

Ƙaramin ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare Clem Agba, ya bayyana damuwa kan tasirin da rashin isassun kuɗi da matsalar tsaro da kuma bambance-bambancen al’adu za su yi wa aikin ƙidayar jama’a da za a yi a ƙasar cikin wannan shakara.

An dai tsara gudanar da ƙidayar ne tsakanin ranakun 29 ga watan Maris zuwa biyu ga watan Afrilun wannan shekara.

Mista Agba ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wata ganawa da ya yi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da da sauran masu ruwa-da-tsaki a Abuja da nufin tattauna ɓangarorin da za su iya kawo tarnaƙi ga aikin ƙidayar.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta fitar da fiye da kashi 60 na kuɗaɗen da ake buƙata domin aikin, inda ya ƙara da cewa yanzu ana jiran masu ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su bayar da nasu kason.

Ganawar dai ita ce ta biyu da jami’an hukumar ƙidaya ta ƙasar ke yi da ƙungiyoyin da za su taimaka wajen gudanar da shirin a shirye-shiryen gabatar daƙidayar jama’ar.

Ɗaya daga cikin maƙasudin ganawar shi ne yadda za a samara kudin gabatar da ƙidayar, inda hukumar ya yi alƙawarin gudanar da komai a bayyane.

Duk da cewa an samu matsalolin tsaro a lokacin aikin gwajin da aka yi a wasu ƙananna hukumomin ƙasar, shugaban hukumar ƙidayar ya kawar da fargabar da wasu ke yi na cewa ba za a yi aikin a wasu sasan ƙasar ba.

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp