Wani karamin yaro dan shekara goma ya nutse cikin kogi a karamar hukumar Buji ta jihar Jigawa.
Gidan talbijin na Channels ya ambato CSC Adamu Shehu, mai magana da yawun rundunar tsaron farin kaya ta Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a jihar Jigawa yana tabbatar da haka a cikin wata sanarwa.
A cewar Adamu Shehu yaron mai suna Sule Ya’u ya je wanka ne a kududdufi cikin kauyen Lelen Kudu tare da abokansa a ranar Asabar.
Ya ce daga bisani bayan nema da aikin ceto na tsawon sa’a biyu an gano gawar yaron, kuma bayan kai shi asibiti likitoci suka tabbatar da cewa ya riga mu gidan gaskiya.
Sassa da dama na jihar Jagawa na fama da ambaliyar ruwan da aka dade ba a ga irinta ba cikin ‘yan shekarun nan.