Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Talata ya bayyana cewa, Najeriya ba za ta iya sake samun wani yakin basasa da ya wargaza kowane bangare na kasar.
El-Rufai ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin rufe kwas din wayar da kan jama’a da aka shirya wa mambobin kungiyar masu yi wa kasa hidima ta 2022 Batch B (Stream 2) da aka tura Kaduna.
Gwamnan ya bukaci matasan da kada su hura wutar rikici da yaki a Najeriya.
El-Rufai wanda Mukaddashin Gwamnan Jihar, Dakta Hadiza Balarabe ya wakilta, ya ce: “Dole ne matasa su tuna cewa, NYSC ta samo asali ne bayan yakin basasar da ya wargaza duk wata kasa ta Najeriya. Yakin ya kasance dabbanci maras bukata wanda ba za mu iya maimaita shi ba.
“Saboda haka dole ne matasan Najeriya su nisanta kansu daga rura wutar rikici da yaki a Najeriya.”