Daraktan kamfen din Bola Tinubu, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana irin tarin dukiyar da Bola Tinubu ya ke da ita, sakamakon cece-kuce da a ke yi a kai.
A wata hira da Jibrin ya yi da gidan talabijin na Channels ya ce, Tinubu tun kafin ya shiga siyasa mai tarin arziki ne, domin ya yi aiki da kamfanin mai na Mobil da wasu manyan kamfanoni.
Ya bayyana cewa, jama’a za su yi mamaki idan ya sanar da cewa Tinubu ya na da hannun jari a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
Ya ce, tushen arzikin shugaban Jam’iyyar APC ta kasa bai taba zama dalilin tada kura ba,inda yace hakan abu ne bayyananne.
Kamar yadda tsohon dan majalisar ya ce, kungiyoyin kasashen duniya sun dade suna bibiyar Tinubu, tun daga rayuwar da ya yi a makaranta, inda ya ce, tsohon gwamnan Legas din ya yi aiki a kamfanin Mobil da wasu kamfanoni kafin ya fada siyasa. Kuma Tinubu bai shigo siyasa a fakiri ba.
“Zan iya tabbatar muku da cewa, duk sanatocin Najeriya babu talaka, kuma ya shigo siyasa a matsayin sanata. Ya na da hanyoyin samun kudi, mutumin nan kasuwanci a jinin sa yake. Ya na kasuwanci tsakanin kasa da kasa. Duk mutanen da ke cece-kuce game da shi sun sani sarai cewa, ya na daukan nauyin hidindimun siyasar sa, ba tare da wani ya tallafa ma sa ba, tun a tsakiyar karni na 19”. In ji Jibrin.