Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya umarci sojojinsa da su dakata da kai hari a masana’antar mulmula karafa ta Azovstal da ke birnin Mariupol da aka yi wa kawanya a Ukraine, yana mai cewa yana son a ci gaba kare ta.
Mayakan Ukraine na karshe a birnin sun buya a masana’antar, kuma rahotanni sun akwai fararen-hula kusan 1,000 da ke cikin mawuyacin hali a can.
Putin ya bayar da umarnin rufe masana’antar yayin tattaunawar da ya yi da Sergei Shoigu, ministan ma’aikatar tsaron kasar, wadda aka watsa a kafafen labarai.
Ya taya kansa murna bisa nasarorin da suka samu a Mariupol bayan Shoigu ya yi ikirarin cewa dakarun Rasha sun kwace birnin.
A baya Shoigu ya shaida wa Putin cewa akwai fiye da mayakan Ukraine 2,000 a cikin masana’antar, wadanda suke cikin dakunan karkashin kasa.