Tsohon Ministan Kwadago da Aiki, Festus Keyamo, ya mayar da martani kan sakamakon kwamitin da Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo ya kafa, domin ya binciki cece-kucen da ke tsakanin Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i ta JAMB da Ejikeme Mmesoma kan sakamakonta na UTME.
Keyamo ya bayyana Mmesoma a matsayin hazikin yarinya, inda ya shawarci al’ummar kasar su yi taka tsantsan kada su halaka ta, inda ya ce abin da take bukata shi ne nasiha, gyara da kuma jagora.
Bincike ya nuna Mmesoma ta ƙirƙiri maki 362 da ta ke nunawa sabanin ingantacciyar maki, 249.
A wata sanarwa da ya fitar ta shafin Twitter da aka tabbatar a ranar Asabar, tsohon Ministan, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya ce da gangan ya jira karshen binciken kafin ya yi tsokaci kan labarin.
Keyamo ya kuma shawarci iyayenta da su kara mata kwarin guiwa da ta yiwa hukumar JAMB da iyalanta da ‘yan Najeriya hakuri, sannan a bar ta ta samu gurbin karatu a bisa hakikanin maki.
Ya rubuta cewa, “Na jira karshen wannan bincike da gangan kafin in yi tsokaci kan wannan mummunan lamari na ‘yarmu Mmesoma Ejikeme.
“Yarinya ce haziki, idan aka yi la’akari da ainihin maki 249. Ya kamata al’umma su yi hattara kar su halaka ta. Abin da take bukata shi ne nasiha, gyara da kuma jagora. Babu shakka ba ta san nauyi da nauyin abin da take yi ba. A matsayinmu na matasa, yawancinmu mun yi kurakuran yara waɗanda ba su taɓa fitowa fili ba.
“Ya kamata iyaye su karfafa mata ta yi hakuri da jama’a ga hukumar JAMB, ga iyalanta da kuma ‘yan Najeriya daga nan sai a ba ta damar samun gurbin karatu a bisa hakikanin maki. Duk wanda har yanzu yana tura wasu ruwayoyi akan wannan batu ba ya taimaka mata da danginta.
“Lokaci ya yi da za a rufe wannan babin mara dadi kuma mu ci gaba. Wannan ita ce rokona.”


