Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga babban bankin Najeriya, CBN, da kada ya dage wa’adin karbar tsofaffin naira, bayan 10 ga watan Fabrairu.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kungiyar yakin neman zaben Atiku ta fitar a ranar Laraba.
Atiku ya ce masu yin magudin zabe na da burin tura CBN ya tsawaita wa’adin zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga Maris domin cimma burinsu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci babban bankin kasar da ya gaggauta binciki matakan da ya sanya a gaba domin tabbatar da zagayowar sabbin takardun kudi na Naira tare da saukaka wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu musamman mazauna karkara.
Karanta Wannan: Obi da Kwankwaso ba barazana ce a gareni ba – Atiku
Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa: “Bai kamata a sake dage tsarin mulkin na Naira ba bayan karewar wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.
“Masu magudin zabe suna neman tura CBN ya tsawaita har sai bayan zabe da sun cimma munanan makircinsu.
“Ya kamata CBN da Fadar Shugaban Kasa su tsaya tsayin daka. Amfanin sabuwar manufar Naira ya zarce kadan daga cikin matsalolin da muke fuskanta.”