Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta ce ba ta daukar ma’aikata.
Hukumar ta kuma gargadi jama’a da su yi hattara da badakalar ayyukan yi.
Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hukumar Mista Femi Babafemi, ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa hukumar na sane da wata buga ta bayyana cewa tana daukar ma’aikata.
“Yayin da muke daukar matakan da suka dace don bankado mutanen da ke da hannu wajen buga wannan labari, an shawarci jama’a da su guji yin zamba.
“Hukumar za ta so ta jaddada cewa babu wani daukar ma’aikata a halin yanzu.
“A lokacin da ya dace, duk wani bayani game da daukar ma’aikata za a raba shi a gidan yanar gizon mu da kuma shafukan yanar gizon mu kawai,” in ji kakakin NDLEA.