fidelitybank

Kar a sake a miƙa Hamdiyya hannun Ƴansanda – Amnesty

Date:

Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya ta soki matakin da hukumomi ke shirin ɗauka na miƙa matashiyar nan da aka gano a jihar Zamfara, Hamdiyya Sharif ga jami’an ƴansanda.

Shugaban ƙungiyar Mallam Isa Sanusi ya shaida wa BBC cewa bayanan da suke samu shi ne kwamishinan ƴansanda jihar Zamfara ya nace sai an mayar da Hamdiyya Sharif ga hukumar ƴansandan Sokoto, maimakon ba ta kulawar likitoci, wanda a cewarsa shi ta fi buƙata a halin yanzu.

”Mu yanzu abin da muka fahimta a taƙaice shi ne kenan an kamata, ko kuma sun riƙe ta”, in ji shi.

Mallam Isa Sanusi ya yi kira ga hukumomin Najeriya su bai wa matashiyar kariya saboda yadda rayuwarta ke cikin ”barazana”.

A yammacin ranar Laraba ne aka gano Hamdiyya Sherif a wani ƙauye cikin jihar Zamfara, bayan ɓatan-dabo da ta yi a ranar Talata a jihar Sokoto.

A bayanan da wata makusanciyar Hamdiyya ta yi wa BBC, ta ce wasu mutane ne suka sace matashiyar tare da yi mata wata allura, lamarin da ya kai ga fita daga cikin hayyacinta, inda daga baya ta tsinci kanta cikin wani daji a jihar Zamfara mai maƙwaftaka.

Sanarwar Amnesty ta ce “yanzu haka rayuwar Hamdiyya Sharif na cikin haɗari, kuma wajibi ne hukumomin Najeriya su ba ta kariya”.

Hamdiyya na fuskantar shari’a a kotu, inda gwamnatin jihar Sokoto, da ke arewa maso yammacin Najeriya ke tuhumar ta da zargin yunƙurin tayar da zaune tsaye bayan ta yi wani bidiyo tana sukar gwamnati kan rashin ɗaukan matakan da suka dace kan matsalar tsaro.

Sokoto na cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan fashin daji masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Ƙauyuka da dama sun yi ƙaura sanadiyyar kashe-kashen wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa duk da ƙoƙarin da gwamnati ta ce tana yi wajen yaki da matsalar.

Amnesty International da lauyoyin Hamdiyya na nuna yatsa ga gwamnatin jihar Sokoto, wadda suka ce tana ƙoƙarin rufe bakin masu suka, lamarin da suka ce ya saɓa tsarin ƴancin fadin albarkacin baki.

thisday newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Har yanzu Tinubu bai nada Jakadun Najeriya ba – ADC

Jam’iyyar ADC ta soki yadda gwamnatin APC ta shugaba...

Har yanzu ina LP kuma ni ne zan iya saita Najeriya – Datti

Datti Baba-Ahmed, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a...

APC ta zama buhun kusa ta gaza a Najeriya – Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya bayyana jam'iyyar...

An fara samun takun saka tsakanin Turkiyya da Najeriya a kan kungiyar Gulen

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta bukaci shugaban kasar...

Arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025 – NBS

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin...

Kamfanonin lantarki za su katse wutar lantarki saboda bashi

Kamfanonin samar da wutar lantarki, sun ce suna iya...

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...
X whatsapp