fidelitybank

Kar a je da Karnuka waje zaɓe -Ƴan Sanda

Date:

Rundunar ‘yan sanda ta ja kunnen masu zuwa da Karnuka ko wasu nau’ikan dabbobi a rumfunan zaɓe musamman a ranar zaɓe.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ya fitar, ta ce sashe na 126 na dokar zaɓe ta 2022 ya bayyana ƙarara cewa yin hakan saɓa doka ne, kuma laifi ne da aka tanadar wa hukunci ƙarƙashin dokar riƙe makami domin razana masu kaɗa ƙuri’a da jami’an zaɓe.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana ɗaukar karnuka a matsayin makamin da masu su ke amfani da su domin razanarwa ko cin zarafi ko raunata jama’a.

”Aƙidar zuwa da karnuka rumfunan kaɗa ƙuri’a da masu zaɓe, ko wasu gungun mutane ke yi ba abu ne da za a lamunta ba, kuma muna kira da a dakatar da yin hakan, saboda ya saɓa da dokar zaɓe domin kuwa hakan na janyo razani da tsoratarwa”, in ji sanarwar.

Daga ƙarshe sanarwar ta gargaɗi masu niyyar zuwa da karnuka ko sauran nau’ikan dabbobin rumfunan zaɓe da su guji yin hakan, saboda a cewar rundunar hakan saɓa dokar zaɓen ƙasar ne.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp