fidelitybank

Kante ya bi sahun Benzema zuwa Al-Ittahad

Date:

N’Golo Kante ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku da Al-Ittihad ta Saudiyya, kamar yadda wata majiya ta sanar wa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Dan kwallon tawagar Faransa ya je kungiyar kwana daya bayan tsohon dan wasan Real Madrid, Karim Benzema ya koma Al-Ittihad.

Kante, mai shekara 32, ya je an auna koshin lafiyarsa daga baya ya saka hannu kan kunshin yarjejeniya, kamar yadda majiyar ta sanar da labarin cewar ba a ba ta izinin bayyana batun daukar Kante ba.

Kante wanda ya bar Chelsea a kakar nan, ya lashe kofin duniya a 2018 a Rasha tare da tawagar Faransa, kuma a halin yanzu yana fama da raunin da ya yi jinyar wata shida.

Majiyar ba ta fayyace kan kudin da Kante ya amince da kunshin yarjejeniyar buga gasar kwallon Saudi Arabia ba.

Ranar Talata Al-Ittihad ta sanar da daukar Benzema, mai shekara 35, shima kan kwantiragin kaka uku, bayan da yarjejeniyar ta kare a bana da Real Madrid.

Benzema da Kante da kyaftin din Argentina, Lionel Messi, na cikin ‘yan kwallo 10 da Saudiyya ta tsara dauka, domin bugawa a gasar tamaula na kasar.

taraba state today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp