Kocin Kano Pillars, Abdullahi Maikaba, ya bayyana shirin ‘yan wasansa na karawar da za su yi da Abia Warriors.
Maikaba ya bayyana hakan ne ga manema labarai na kungiyar bayan atisayen da suka yi da yammacin ranar Asabar a Umuahia.
Kwararren kocin ya bayyana cewa, kungiyarsa za ta iya kwace nasarar farko da suka yi a waje da Ochendo Boys.
Ya bukaci ’yan wasan da su ci gaba da mai da hankali a duk lokacin da suke karawar.
Za a yi wasan ne a filin wasa na garin Umuahia.
Kano Pillars ta doke abokiyar hamayyarta Katsina United a makon da ya gabata, inda ta samu nasarar zama ta farko a kakar wasa ta bana.
Sai Masu Gida a halin yanzu ta na matsayi na 11 akan tebur.