Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Fc, ta dauki wasu ‘yan wasa uku kan shirye-shiryensu na tunkarar kakar wasa ta NPL na 23/24 mai zuwa.
Ƴan wasan akwai, Ibrahim Abdullahi, tsohon dan wasan kwallon kafa na gaba, kuma dan wasan Samba Kurna, ya rattaba hannu a kwantiragin shekara daya da kungiyar Sai Masu Gida.
Sa’idu Adamu (Dan wasan tsakiya) ya rattaba hannu a kwantiragin shekaru biyu da Sai Masu Gida daga Enugu Rangers.
Adams Musa (Dan wasan gaba), ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu da Kano Pillars Fc daga Enugu Rangers.


