Sani Faisal ya koma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars kan kudi da ba a bayyana ba.
Sani ya hade kai da kungiyar Sai Masu Gida, bayan dan takaitaccen lokaci da kungiyar Al-Wahda SC a gasar Omani.
Ya buga wasanni shida a bangaren Larabawa.
Dan wasan baya na hagu ya buga wasan aro da Kwara United a kakar wasan data gabata.
Dan wasan mai shekaru 27 ya buga wasanni biyu a Super Eagles a gida a shekarar 2022.
Sani ya kuma buga wa Abuja FC a baya.


