Kungiyar Kano Pillars ta daukaka kara kan tarar da hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta ci ta mata.
An ci tarar Sai Masu Gida Naira miliyan 1 kan laifin cin zarafi da magoya bayanta suka yi a wasan da suka yi da Rivers United a filin wasa na Sani Abacha a ranar Lahadin da ta gabata.
Jami’in yada labarai na kungiyar ta Kano Pillars Idris Malikawa ya bayyana cewa kungiyar ta rubutawa hukumar NPFL wasika domin ta sake duba matakin da suka dauka.
Malikawa ya kara da cewa kungiyar ta kuma roki NPFL da a yi musu sassauci.
“Kano Pillars ta bukaci hukumar kula da gasar ta sake duba shawarar ta,” kamar yadda ya shaidawa manema labarai.
Your message has been sent
“Kano Pillars kuma ta roki NPFL da ta yi musu sassauci saboda ayyukan magoya bayanmu.”


