fidelitybank

Kano: Na dauki wasu nauyin ayyukan kungiyar Boys Scout – Hamisu Chidari

Date:

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Hamisu Ibrahim Chidari ya jijinawa kungiyar bayar da agaji ta Boys Scout ta Jihar Kano bisa kokarinta na inganta tsaro da lafiyar alumma.

Kakakin Majalisar ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar a Majalisar Dokokin, ya na mai bayyana Kungiyar ta Boys Scout da cewar dadaddiyar kungiya ce da ta yi fice wajen bayar da gudunmawa a harkokin cigaba a birane da karkara.

Ya kuma ja hankalisu da su rike wannan kambun na su ta hanyar kara jajircewa a kan ayyukansu.

Cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran majalisar, Uba Abdullahi ya sanyawa hannu a ka kuma rabawa manema labarai, sanarwar ta ce Chidari ya sha alwashin tallafawa Kungiyar akan wadansu ayyuka da ta bijiro da su, domin bunkasa harkokin Kungiyar.

A jawabinsa, Shugaban Kungiyar a Jihar nan, Alhaji Baffa Muhammad ya ce”Mun kawo ziyara Majalisar Dokokin ne, domin inganta zumunci tare da yabawa Kakakin Majalisar bisa yadda Majalisar ke aiki tukuru, domin inganta rayuwar alummar Jihar nan”.

Haka kuma ya godewa Kakakin Majalisar bisa kokarinsa na daukar dawainiyar wasu daga cikin ayyukansu.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...

Tarayyar Turai tamince da ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da ƙaƙaba wa Rasha...

Gwamnan Filato ya zargi Jami’ai da kin kama ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Filato ta zargi jami'an sojojin ƙasar da...

Za a yi wa Buhari addu’a a Abuja

Gwamnatin Tarayya za ta jagoranci gudanar da taron addu'o'i...

Buhari ya ban umarni na kula da Talakawan Najeriya – Peter Obi

Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce,...

Sojojin hadin gwiwa sun hallaka ‘yan Boko Haram a tafkin Chadi

Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a...

Na yi rashin aboki na gari kuma Najeriya ta rasa mutumin kirki – Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na ci gaba da alhinin...

Shettima ya jagoranci yi wa Buhari addu’o’i na musamman a Daura

An gudanar da addu'o'i na musamman don neman gafara...

Isra’ila ta kashe mana fararen hula – Syria

Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya zargi Isra'ila da kai...
X whatsapp