Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta fitar kan alƙaluman makon farko na mutanen da suka nuna aniyar yin rajistar zaɓe ta intanet sun nuna cewa al’umma ba su fito sosai ba a yankin arewacin ƙasar domin yin rajistar.
Alƙaluman da hukumar ta Inec ta fitar a jiya Litinin sun nuna cewa jihar Osun ce ta fi yawan mutanen da suka nuna aniyar yin rajistar, inda take da yawan mutane 393,269, jihar Legas ke biye mata da mutum 222,205 sai kuma jihar Ogun mai yawan masu son yin rajista 132,823.
A arewacin Najeriya, Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar ne ke da mafi yawan mutanen da suka nuna aniyar yin rajista, inda take da mutum 107,683, sai jihar Kaduna mai mutum 61,512 yayin da jihar Kogi ke biye mata da mutum 58,546.
Jihar Kano wadda ta fi kowace yawan al’umma a Najeriya na da yawan waɗanda suka nuna aniyar yin rajistar zaɓe 10,166 ne, Adamawa kuma na da 2,115 kacal.
Sai dai idan aka duba ƙasar baki ɗaya za a ga cewa yankin kudu maso gabashin ƙasar shi ne ya fi ƙarancin mutanen da suka nuna aniyar yin rajista a makon na farko.
Jihar Enugu na da mutum 484, Imo 481 sai kuma jihar Ebonyi mai mutum 261 kacal.
A ranar 18 ga watan Agusta ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta buɗe shafinta na intanet domin mutane su nuna aniyar yin rajistar katin zaɓe.
Alƙaluman na Inec sun nuna cewa ya zuwa ranar Lahadi 24 ga watan na Agusta an samu mutum miliyan 1,379,342 waɗanda suka nuna sha’awar yin rajistar ta shafin intanet.
Ya zuwa yanzu alƙaluman na Inec sun ce mata ne waɗanda ke gaba a yawan wadanda suka nuna aniyar yin rajista a fadin ƙasar, inda suke da kashi 52.04% yayin da maza ke da kashi 47.96%.
Daga nan sai hukumar ta sanar da cewa ta buɗe rumfunanta a fadin ƙasar domin bai wa mutane damar zuwa ƙafa-da-ƙafa domin yin rajista.
Aikin yin rajistar zaɓen na zuwa ne gabanin babban zaɓen shekara ta 2027, inda tuni jam’iyyu da kuma masu neman takara suka fara shiri.
Yanzu haka dai ƙasar ta Najeriya mai yawan mutum sama da miliyan 200 na da mutane miliyan 93,469,008 da suka yi rajistar zaɓe a faɗin ƙasar.