Cibiyar kare hakkin jama’a ta Civil Society Legislative Advocacy Centre, CISLAC, ta ce jihohin Kano da Jigawa ne ke kan gaba a jerin jihohin da ke shan taba a Najeriya.
Babban jamiāin tsare-tsare na CISLAC, Solomon Adoga ya bayyana haka a wajen taron kwana daya da masu ruwa da tsaki kan harajin taba sigari a jihar Jigawa, wanda CISLAC ta shirya tare da tallafin Tax Justice Network.
Ya ce an yi hakan ne don a rage yawan shan taba a jihar, musamman a tsakanin matasa.
A cewarsa, āAbin takaici ne yadda bincike ya nuna Kano/Jigawa ce kan gaba a jerin jihohin da ake shan taba a Najeriya, yayin da akasarin masu amfani da taba matasa ne, wasu kuma ba su kai shekaru kanana ba.
“Don sarrafa shan taba, dole ne gwamnatin jihar ta amince da kuma samar da dokar hana shan taba sigari (2015) da kuma manufofin harajin taba don ceton rayuwar matasan mu wadanda za su zama shugabanni na gaba.”
Ya kara da cewa makasudin yin cudanya da muāamala da masu ruwa da tsaki kamar shugabannin gargajiya da na addini da kungiyoyin matasa da kungiyoyin farar hula da kuma kafafen yada labarai shi ne don a taimaka wajen wayar da kan jamaāa kan illolin da ke tattare da shan taba, tare da bayar da shawarwari ga majalisun dokoki da na zartaswa. don yin gida da kuma bin dokokin.