Cibiyar kare dimokuradiyya da kare hakkin dan Adam ta CEDEHUR, ta ayyana jihar Kano ta fuskar sha’anin mulki a matsayin koma baya, kuma mafi karanci a aiwatar da aiki a kasar nan, tun bayan da sabuwar gwamnati ta hau mulki a watan Mayun 2023.
Cibiyar ta yi wannan ikirarin ne a ranar Talatar a Abuja, yayin da take gabatar da rahotonta na kashi uku kan yadda ake gudanar da sha’anin mulki a jihohi 18 tare da sabbin gwamnoni.
Cibiyar ta ce an gudanar da tantancewar ne bisa gaskiya da rikon amana da ingancin wadanda aka nada da kuma tasirin manufofin da suka shafi al’ummar jihohin 18.
Da yake jawabi a madadin Cibiyar, Amb. Adebayo Lion Ogorry ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, Kano ta kasance a matsayin mafi kasa ta fuskar shugabanci na gari, yana mai zargin cewa gwamnati mai ci ta mayar da hankali ne kan tsarin siyasa mafi koma baya.
Ya kuma ce, Kano na daya daga cikin Jihohin da Gwamnansu ya samu matsala ta bangarori da dama.
Daga kididdigar da ake da ita, jihar ta tsunduma cikin harkokin siyasa da suka shafi harkokin mulki.
Daily Post ta rawaito cewa, gwamnan jihar yana da ra’ayin magance matsalolin zamantakewa da tattalin arzikin jihar.
Sai dai Ogorry ya kara da cewa, nade-naden mukaman da aka yi a Kano, an yi ne bisa la’akari da gudunmawar da mutanen suka ba shi a siyasa ba wai domin saboda gogewa ko cancantar su ba.