Darakta a masana’antar fina-finan Kannywood, Nura Mustapha Waye, ya rasu.
An sanar da rasuwarsa a safiyar Lahadi, bayan an wayi gari an ga ya rasu.
Nura dai ya kasance daraktan fina-finai da dama ciki har da shirin nan mai dogon zango na Izzar So.
Tuni dai wasu daga cikin jaruman Kannywood suka yi ta’aziyya ga Nura ,inda suka yi addu’ar Allah ya yi masa gafara.